Doki |
---|
Doki wata dabbace mai kafafuwa hudu (4), wacce take da girma da karfi tana kuma da gashi, amma mara yawa. Doki na da bindi mai tsawo kuma yana da gudun gaske. Haka kuma ana hawan doki da kuma wasa da shi. Sai dai ba a cin naman doki [1][2] A kasa hoton wani doki da kuma ta macen doki wato (godiya) tana shayar da ɗanta.
.
Doki yana da amfani a gurin yan adam, suna amfani da shi tin a zamanin da wajen tafiye-tafiye da wasanni da noma da yaki da kuma ban ruwa a gona. Sannan kuma ana sanya wa doki linzami da abin hawa domin mutum ya hau saman kansa ya yi tafiya, sannan ana amfani da su a filin yaki.
Tin asali ɗan adam yana hawa doki domin bukatun kansa.
A al'adar mutane suna amfani da doki a lokacin bukukuwa da kuma wasannin gargajiya irinsu; tseren doki da hawan sallah da hawan daba da kuma gasar sarrafa doki.