Jihar Edo Jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya.[1] Babban birnin jihar shi ne Benin. Dangane da ƙidayar shekara ta 2006, Jihar ita ce ta shida a yawan jama'a da adadin mutane kimanin 3,233,366.[2] Edo ita ce ta 22 a faɗin ƙasa a Najeriya.[3] Babban birnin jihar shi ne Benin City, ita ce birni ta hudu a girma a Najeriya, kuma ta ƙunshi cibiyar masana'antun roba a Najeriya.[4][5] An ƙirƙire ta a shekarar 1991, daga tsohuwar Jihar Bendel, kuma ana kiranta da kuma suna "Heart beat of the Nation" (bugun zuciyan ƙasa).[6]
Yankunan Jihar Edo a yau sun haɗa iyaka da masarautun da dauloli da aka kafa tun a ƙarni na 11 miladiyya, harda Masarautar Benin.[8] A shekarar alif 1897, Daular Burtaniya ta ƙaddamar da wata azzalimar ziyara ga yankin Benin, inda suka tarwatsa tsaffin biranen Edo, inda suka haɗe su a cikin yankin da ta zamo Yankin mulkin mallaka na Kudancin Najeriya.[9][10]
Edo jiha ce dake ɗauke da mutane iri-iri musamman Harsunan Edoid da kuma Mutanen Edo ko Bini,[11]Esan, Kabilar Owan, Afemai.[12] Harshen da yafi fice daga cikin yarukan Edo shine Yaren Edo wanda akae yawan amfani dashi a Birnin Benin.[13] Mafi yawa mutanen Jihar mabiya addinin Kiristanci ne. Turawan mishanari na Portugal suka kawo addinin a yankin a ƙarni na 15. Akwai 'yan tsirarun mabiya addinin Musulunci da addinan gargajiya.[14]
Yankin Yamma ta Tsakiya, Najeriya yanki ne a Najeriya a tsakanin shekarun 1963 zuwa 1991. Kuma ana kiranta da Jihar Bendel daga shekarar 1976. An ƙirƙiri jihar a watan June 1963, daga yankin gundumomin Benin da Delta na Yankin Yammacin Najeriya, kuma babban birninta shi ne Benin City.[15] An canza mata suna zuwa gunduma a 1966, sannna kuma a 1967 lokacin da aka rarraba sauran gundumomin zuwa jihohi da dama, ta tsaya a matsayin yanki, kafin daga bisani ta zamo jiha.[16]
A lokacin Yaƙin basasar Najeriya, sojojin Biyafara sun kai wa sabuwar jihar Yankin Yamma ta Tsakiya hari, wacce ta haɗa hanya da Lagos, a wata yunkuri na tilasta kawo karshen yakin. A yayin wannan fafatawar, an sanya wa jihar suna ''Jamhuriyar Benin gabanin sojojin Najeriya su sake ƙwato yankin. Jimhuriyar ta zo ƙarshe na tsawon yini ɗaya bayan sojojin Najeriya sun kwace birnin Benin City. An ƙirƙiri jihar Edo a ranar 27 ga watan Augustan 1991, a lokacin da aka raba Jihar Bendel zuwa jihohin Edo da Delta.[17][18]
Tare da Birnin Benin a matsayin babban birnin jihar, yawan mutanen garin sun kai kimanin mutum miliyan 8.[19] Jihar ta kunshi muhimman kabilu guda hudu sune: Kabilar Edo (mutanen Bini, Owan, Esan, Afemai (Etsakọ da kuma Akoko-Edo). A jihar akwai mutane daga yankuna da dama daga sassa daban daban na duniya. Birnin bini yana da tarihin zama daya daga cikin yankunan da Turawa suka zauna a zamanin ziyarar su Nahiyar Afirka daruruwan shekaru da suka gabata. Wasu daga cikin wadannan yankuna sun zamo wuraren ziyaran buda idanu a yau.[20]
Muhimman kabilun Jihar Edo sun hada da kabilun Bini, Etsako, Esan, Owan da kuma kabilar Akoko Edo.[19] Yawancin wadannan Kabilu sun samo asalli ne daga babban birnin Benin City, a dalilin haka harsunansu sun bambanta ne dangane da nisansu da babban birnin. Kabilar Bini sun mamaye kananan hukumomi guda bakwai daga cikin kananan hukumomi 18 dake jihar kuma sun kwashe kaso 57.54% na yawan mutanen Jihar. Sauran kuma: Esan (17.14%), Etsako (12.19%), Owan (7.43%), da kuma Akoko Edo (5.70%).[19] Amma kuma akwai yarukan dake zaune a yankunan Akoko Edo, su kuma Itsekiri na zaune a yankin Ikpoba-Okha, da kuma harsunan IjawIzons, Urhobos dake zaune a kananan hukumomin Ovia ta Arewa maso Gabas da Kudu maso Yamma da kuma yankunan iyakokin jihar. Har wayau, ana samun mutanen Ibo a yanki Igbanke(Ika) dake karamar hukumar Orhionmwon.[21]
Sashen Shari'a itace mataki na uku na gwamnatin Jihar Edo, wacce ke da alhakin zartar da shari'a da kuma sasanta rigingimu na al'umma da kuma masu laifi a jihar. A ranar 16 ga watab Mayun 2021 ne, Gwamna Obaseki ya rantsar da Mai Shari'a Joe Acha a matsayin a matsayin Alkalin Alkalai na rikon kwarya a Jihar Edo, bayan mai shari'a Esther Edigin ya ajiye aiki.[25]
Godwin Obaseki ne gwamnan jihar Edo na yanzu kuma an rantsar da shi a ranar 12 ga watan Nuwamban, 2016.[26] Mataimakinshi kuma shine Comrade Philip Shaibu.[27]
Wuraren ziyara na Jihar Edo sun hada da; Mutum-mutumin Emotan dake cikin Birnin Benin, koramar Ise, da wurin shakatawa na gabar Kogin Niger wato Agenebode. Etsako-East; Mike Akhigbe Square dake fugar, Ambrose Alli Square, Ekpoma, River Niger Beaches da ke Ilushi, BFFM Building dake Ewu, Igun Bronze Caster da ke Igun Street a birnin Benin City, Kwalejin numa da kiwon halittun ruwa (Agriculture and Aqua Culture Technology, Agenebode), Okpekpe da tsaunukan ta da wuraren kallo, tsaunin Usomege Hills, Apana-Uzairue, Somorika hills da ke Akoko Edo inda akwai wurin bude ido da gwamnati ta a shirya a Ososo da kyawawan wuraren kallon.[36][37]
Jihar tana samar da man fetur[38] da sauran ma'adanai kamar farar kasa da dutsen kwaru. Jihar tana da kamfanin siminti a Okpilla.[39] da kamfanin fulawa a Ewu wanda ke kawo karshe.[39]
Godwin Obaseki, Tsohon chiyaman na jiha na kungiyar harkokin tattalin arziki kuma Gwamnan Jihar Edo na yanzu[71][72]
Jeffrey Obomeghie, Babban jami'i na asibitin International Hospitality Institute da marubuci[73]
Erhabor Emokpae, wanda ya fara fasaha na zamani a Najeriya[74]
Admiral Mike Akhigbe, tsohon mataimakin shugaban kasa na Federal Republic of Nigeria.[75]
Dele Giwa, dan jarida a Najeriya, edita kuma wanda ya kirkiri mujallar Newswatch.[76][77]
Senator Albert Legogie, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa na Jamhuriya ta Uku kuma mafarin "Board of Trustees" na Peoples Democratic Party (PDP).[78]
Pa Michael Imoudu, shugaban labour kuma and founder of the Nigeria state,[79]
Chief Anthony Enahoro, dan adawa da mulkin mallaka kuma mai and pro-democracy activist and politician[103][104]
Professor Festus Iyayi, marubucin littattafai kuma dan Afurka na farko da ya fara lashe lamban yao na Commonwealth Writers Prize[105][106]
Odia Ofeimun, mahikyanci kuma tsohon shugaban Association of Nigerian Authors[107][108]
Dr Abel Guobadia, mai ilimantarwa kuma tsohon jakadan Najeriya da Republic of Korea, tsohon Chairman Independent National Electoral Commission (INEC)[109][110]
Kamaru Usman, kwararren dan damben mixed martial arts wanda aka baiwa kwantiragin Ultimate Fighting Championship, kuma welterweight champion.[139]
Yakubu Ayegbeni, tsohon kwararren dan wasan kwallon kafa[140][141][142]
Rema (Nigerian musician), mawaki wanda ya sa hannu da Mavin Records,[143]
Philip Shaibu (haihuwar 1 December 1969, a Kaduna) tsohon dalbi a University of Jos alkali ne a Najeriya, dan siyasa kuma dan kasuwa. Shine mataimakin gwamnan Jihar Edo na yanzu .[144]
Eghosa Asemota Agbonifo, politician, coordinator of Michael Agbonifo shoe a child foundation[145]
Prof T. M. Yesufu, wanda ya fara zama Vice-Chancellor a Jami'ar Benin, economist.[146][147]
Odion Jude Ighalo, kwararren dan wasan kwallon kafa.[148]
Helen Paul, 'yar barkwanci kuma jaruma kuma an santa da Tatafo. ta kasance fuskar Telecom consumer na Nigerian Communications Commission (NCC).[165][166]
Lancelot Oduwa Imasuen, darekta kuma furodusa a Nollywood. Ya kirkiri makarantan fim na farko a Benin Igbinedion University, Okada, Jihar Edo.
Hon. Joe Edionwele, dan siyasa kuma dan majalisa a majalisa ta 8 da ta 9 National Assembly, Nigeria mai wakiltar mazabar Edo ta Tsakiya.
Prof. Eghosa Emmanuel Osaghae, farfesa akan harkokin siyasa a Jami'ar Ibadan, Jihar Oyo, Najeriya. ya rike matsayin Vice Chancellor a Igbinedion University, Okada tsakanin 2004-2018. A shekarar 2019, ya kasance shugaban Claude Ake a Jam'iar Uppsala da ke Sweden. A shekara ta 2017, Professor Osaghae ya koyar da siyasa da zamantakewa a Van Zyl Slabbert, Jam'iar Cape Town South Africa. A yanzu yana bin sahun MacArthur. Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi matsayin Director General na Nigerian Institute of International Affairs (NIIA).
↑"Nigeria Census - Nigeria Data Portal". nigeria.opendataforafrica.org. Retrieved 2021-07-08.
↑"World Gazetteer: Nigeria - administrative divisions (per geographical…". archive.ph. 2013-01-05. Archived from the original on 2013-01-05. Retrieved 2022-05-12.
↑"Benin City | History & Facts". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-07-09.
↑Obinyan, T. U. (September 1988). "The Annexation of Benin". Journal of Black Studies. Sage . 19 (1): 29–40. doi:10.1177/002193478801900103. JSTOR 2784423. S2CID 142726955.
↑Koutonin, Mawuna (2016-03-18). "Story of cities #5: Benin City, the mighty medieval capital now lost without trace". the Guardian. Retrieved 2021-07-10.
↑"Edo" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2020-05-30.
↑Refugees, United Nations High Commissioner for. "Refworld | Nigeria: Esan ethnic group; whether it is a sub-group of the Yoruba; religions practised; whether members of this ethnic group engage in Ogboni practices". Refworld. Retrieved 2021-03-15.
↑"Edo language, alphabet and pronunciation". omniglot.com. Retrieved 2021-03-15.
↑"Benin kingdom/Edo state Religions". www.edoworld.net. Retrieved 2021-03-15.
↑"About Edo". Edo State. 2019-07-11. Retrieved 2021-07-08.
↑"Edo state: The heartbeat of the Nation". Channels Television. Retrieved 2021-07-09.
↑Bondarenko, Dmitri M.; Roese, Peter M. (1999). "Benin Prehistory: The Origin and Settling down of the Edo". Anthropos. 94 (4/6): 542–552. ISSN 0257-9774. JSTOR 40465021.
↑ 19.019.119.2"About Edo". Edo State. 2019-07-11. Retrieved 2021-07-10.
↑"About Edo". Edo State. 2019-07-11. Retrieved 2021-07-09.
↑"Daily, Peoples (2020-07-17). "Edo: Igbo community in Edo declare support for Obaseki". Peoples Daily Newspaper. Retrieved 2021-07-10.
↑Seibert, Uwe (24 April 2000). "Languages of Edo State". University of Iowa. Archived from the original on 13 December 2007. Retrieved 10 November 2007.
↑ 29.029.1"Full List of Tribes in Edo State Nigeria | AllNigeriaInfo". Retrieved 2022-01-31.
↑"Benin: City of tradition and culture". Vanguard News. 2011-10-27. Retrieved 2021-07-10.
↑"Full List of Tribes in Edo State Nigeria | AllNigeriaInfo". Retrieved 2022-01-31.
↑"Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 10 January 2020.
↑"Edo 2020: Group vows to boycott poll if Muslim candidate is not fielded". Tribune Online. 2020-03-23. Retrieved 2022-05-12.
↑"Benin: City of tradition and culture". Vanguard News. 2011-10-27. Retrieved 2022-05-12.
↑"Edo State". NigeriaGalleria. Retrieved 28 December 2009.
↑"70 Exciting Tourist Spots". OnlineNigeria. Retrieved 28 December 2009.
↑Ogbeifun, Greg U (April 2006). "Importance of a Sea Outlet for Edo State". Retrieved 10 November 2007.
↑ 39.039.1"CEMENT MANUFACTURING /PRODUCTION IN NIGERIA. A CASE STUDY OF EDO CEMENT FACTORY, UKPILLA, EDO STATE". NAU :: Open Educational Resources. Retrieved 2022-08-15.
↑"Natural Resources – Welcome To The Embassy of Nigeria". Retrieved 2022-05-09.