Jigawa | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Dutse | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 6,000,163 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 259.14 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 23,154 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | jihar Kano | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar zartaswa ta Jihar Jigawa | ||||
Gangar majalisa | Zauren majalisar dokokin jihar Jigawa | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 720001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-JI | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | jigawastate.gov.ng |
Jigawa Jiha ce dake Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriya. An kafa jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991[1] daga jihar Kano a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Babban birnin jihar shi ne Dutse.[2] Jigawa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da jihar Yobe a arewa maso gabas, Bauchi a kudu maso gabas da kudu, Kano a kudu maso yamma da kuma Katsina a arewa maso yamma.
Tattalin Arzikin Jihar Jigawa yana da alaƙa da ayyukan bangaranci na yau da kullum tare da aikin noma a matsayin babban aikin tattalin arziki. Fiye da kashi 80% na al'ummar jihar sun tsunduma cikin noma da kuma kiwon dabbobi. Ana gudanar da ciniki da kasuwanci na kanana da matsakaita, musamman a harkar noma, kiwo da sauran kayayyakin masarufi. Jigawa ta shahara a fannin Noma da kiwo, Manyan amfanin gona na jihar sun haɗa da gyada, dawa, gero, shinkafa, Ridi, da kuma Zobo (yakuwa).a fannin kiwo kuma, Kiwon shanu, awaki, da tumaki ya yaɗu sosai a jihar.
Jihar Jigawa Tana da fadin ƙasa kimanin muraba'in kilomita dubu ashirin da uku, da ɗari da hamsin da huɗu (23,154) da yawan jama’a kimanin miliyan biyu da dubu ɗari takwas da ashirin da tara da ɗari tara da ashirin da tara (kidayar yawan jama'a shekara ta 1991). Babban birnin jihar shi ne Birnin Dutse.
Jihar Jigawa tana da iyaka da jihohi hudu dake Najeriya, su ne: jahar Bauchi, jahar Kano, jahar Katsina,da kuma Yobe. [3] [4].
Jigawa wani sassa ne na kasar , a Arewa maso yammacin Nigeria .Hausa hausawa sune mafi rinjaye a jihar Jigawa sannan akwai Fulani [5]da Mangawa da Badawa da Ngizimawa wadanda yarukan kanuri ne. Mafiyawancin su suna a kananan hukumomin Birniwa, Guri da Kiri kasamma.
.
Tsarin masarautar gargajiya a Jihar ya kasu zuwa masarautu guda biyar kowacce tana da basaraken gargajiya mai suna sarki (sarki) da yake gudanarwa tare da Hakimai da dagatai da masu unguwanni suna taimaka musu. Sarakuna da Hakimai, ba kamar sauran masu rike da madafun iko ba, ba sa gudanar da harkokin siyasa, sai dai a matsayin masu kula da al’adu da masu ba gwamnati shawara kan harkokin gargajiya da na addini. Duk sarakunan masu rike da mukamai ne ajin farko.
https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Jigawa_State.
Wannan jerin sunayen dake gasa, shine jerin sunayena Shuwaga bannin Gananon Hukumomi guda ashirin da bakwai (27) dake a Jihar Jigawa a wannan shekara ta alif dubu biyu da ishirin da hudu (2024.)
Jihar Jigawa tana da ƙananan Hukumomi guda ashirin da bakwai (27). Kananan Hukumomin kuwa su ne:
Ma'adanai da ake samu sun hada da;
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
/gallery>